A cikin jaruman Kannywood ina son inyi aiki tare da Rahama Sadau – Inji fitacciyar jarumar Nollywood

103


Fittaciyar jarumar nan ta masana’antar shirya fina-finai na Kudu wato Nollywood, Linda Osifo ta bayyana aniyar yin wasa tare da korarriyar jarumar hausa Rahama Sadau.
A cewar jarumar, Rahama Sadau yar fim ce wanda ke cike da tarin basira da kuma kwarewa sosai a fannin shirya wasa.
Ta bayyana haka yayin da kai ziyara ta musamman da jaridar Pulse a makon da ya gabata.
Linda Osifo tace fitowar wasu jaruman kannywood a fina-finan nollywood yana taimaka wajen bunkasa masana’antar shirya fim na kasar baki daya.
Jarumar wanda tayi fice a fina-finai daban daban na dandalin nollywood tace hakika jaruman Kannywood na cike da basira kuma nan ba da dadewa tana fatan zata yi aiki da wasu daga cikin su.
Linda wanda asali yar kabilar Ishan ce dake nan jihar Edo tace zata so ta koyi yaren hausa domin yana cikin yarurruka da take neman iyawa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.