_TSAKANI KAFIRI DA MACE MUSULMA, WA ZAN ZABA? Dr Zarewa

252

*_TSAKANI KAFIRI DA MACE MUSULMA, WA ZAN ZABA?_*

*Tambaya*
Assalamu Alaikum. Na karanta post din da kayi akan Shugabancin Mata, inda ka nuna bai halatta mace ta yi shugabanci ba in ba na gidanta ba, Ina so ka dan yi mana Karin bayani idan aka samu takarar shugabanci tsakanin Kafiri da kuma Mace Musulma, wanne ya kamata mutane su zaba a matsayin Shugaba?

*Amsa*
To dan’uwa amsa wannan tambayar yana da wahala, saboda ban ga littafin da ya tattauna mas’alar ba, amma dai na nemi taimakon amsa tambayar wajan babban malaminmu Prof. Muhd Sa’ad Al-yuby, don haka ga bin da zan iya cewa:
Farko dai zaben kafiri haramun ne, saboda fadin Allah madaukakin sarki “Kuma Allah bai sanya wata hanya ba ga kafirai akan muminai” Nisa’i aya ta: 141, hakan sai ya nuna bai halatta musulmai su sanya kafiri ya mulke su ba, Kamar yadda zaben mace a matsayin shugaba shi ma haramun ne saboda hadisin Abu-bakrah inda Annabi s.a.w. yake cewa; “Duk mutanen da suka sanya mace ta zama shugabarsu, to ba za su rabauta ba” kamar yadda Bukhari ya rawaito shi a hadisi mai lamba ta: 4425, Ibnul-kayyim yana cewa: kore rabauta dalili ne da yake nuna haramcin abu. Bada’i’ul-fawa’id 4\812.

Saidai kamar yadda malaman shari’a suke cewa: duk lokacin da abubuwa biyu haramtattu suka hadu, ya zama dole sai an aikata daya daga ciki, to sai a dauki wanda ya fi saukin haramci a aikata.

Idan muka kalli manufar shugabanci a musulunci, za mu ga ta kunshi : jagorancin mutane da kuma tsayar da addini, wannan manufar za ta fi tabbatuwa idan aka zabi mace musulma, fiye da kafiri Crister.

Don haka mutukar matar tana da kokari wajan addini, to ita ya fi kamata a zaba, ba don kasancewar ya halatta a zabe ta ba, sai don kawai hakan ya fi saukin haramci, kuma babu yadda za’a yi sai a zauna babu shugaba.

Allah ne mafi sani.

07/01/2015

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Comments are closed.