_MATAR DA BA TA DA AURE, ZA TA IYA SANYA TURARE TA FITA UNGUWA?

269

*_MATAR DA BA TA DA AURE, ZA TA IYA SANYA TURARE TA FITA UNGUWA?_*

*Tambaya*
Assalam malam muna san karin bayani akansa turare gamata sufita, wani malami yace wadda ba matar aure ba zata iya sawa?

*Amsa:*
Wa’alaikum assalam, To ‘yar’uwa ya *HARAMTA* ga mace Baliga ta sanya turare, ta fita unguwaa, saboda fadin Annabi ﷺ: “Duk matar da ta sanya turare, ta wuce ta wani majalisi, to ta zama mazinaciya, kamar yadda Abu dawud ya rawaito.
A wani hadisin kuma yana cewa: “Duk matar da ta sanya turare, kar ta halarci sallar Isha tare da mu.

Nassoshin da suka gabata suna haramta sanya turare ga mace balagaggiya idan za ta fita, kuma ba su bambance tsakanin matar aure ba da budurwa ko bazawara, wannan sai ya nuna gamewarsu ga dukkan mata wadanda sharia ta hau kansu, tun da ba’a samu abin da ya kebance wasu nau’i ba, sannan kuma an haramta sanya turaren ne: saboda yana kaiwa zuwa tada sha’awar Maza, wannan kuma baya bambanta tsakanin matar aure da wacce ba ta yi ba.

Amma za ta iya sanyawa ta zauna a gida mijinta ya ji kamshi, in ta yi hakan za ta samu lada. Haka ma budurwa, za ta iya sanyawa a tsakanin ‘yan’uwanta mata, ko gaban muharramanta wadanda ta san ba za su yi sha’awarta ba.

Allah ne mafi sani.

22/6/1437
1/4/2016

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Comments are closed.